Labarai
Rahoto : Nazari kan wasanni na gida tana ketare
Daga Abubakar Tijjani Rabiu da Safara Tijjani
‘Yar wasan kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Falcons dake wasa a kungiyar kwallon kafar mata ta Barcelona dake kasar Spaniya, Asisat Oshoala, ta ja hankalin hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) wajen bukatar karbar bakuncin gasar cin kofin Afrika ta mata da za ayi a shekarar da muke ciki ta 2020.
Tuni dai kasar Congo ta janye aniyarta na son daukar nauyin bakuncin gasar a wannan shekarar bisa rashin kudi da kasar ke fuskanta.
Asisat Oshoala da ta samu nasarar lashe kyautar zakarar ‘yar wasan Afrika ta shekarar da ta gabata ta 2019, kuma ta lashe kyautar karo hudu, wanda ake ganin idan kasar nan ta dauki damar gudanar da gasar zai kara fito da martabarta a idan Duniya.
A nan kuma kungiyar kwallon hannu ta kasa ta fara gudanar da gasar cin kwallon hannu ta Afrika da rashin nasara.
Najeriya dai ta yi rashin nasara ne da ci 30-24, da 17-10 a zagayen farko na gasar, inda ta yi rashin nasara a zagaye na biyu da ci 17-10, da kuma 14-13, a hannun kasar Angola a jiya, wasan da ya gudana a filin wasa da ke birnin Tunis a kasar Tunisia.
Idan muka tsallaka turai Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, ta yi ikirarin za ta kawo karshen jerin gwanon nasarar da Liverpool ke yi karkashin gasar Firimiya, bayan da United ta bayyana kanta a matsayin Club guda da ka iya samun nasara akan Liverpool har gidanta yayin wasansu na ranar Lahadi mai zuwa.
Manajan na Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya bayyana cewa ba abin mamaki ba ne, nasarar United akan liverpool idan aka yi la’akari da yadda kungiyoyin biyu suka yi canjaras da kwallo 1-1 cikin watan Oktoba shekarar da ta gabata.
Sai dai duk da kasancewar United a matsayin babbar abokiyar hamayyar Liverpool, ba lallai kalaman na Solsha ya faru ba, la’akari da cewa Liverpool din wadda rabon da ta yi rashin nasara a wasa tun cikin watan Janairun bara a hannun Manchester city,
Shi kuwa tsohon dan wasan Barcelona Xavi Hernandez ya ce, dalilin da ya sa bai karbi aikin horas da Barcelona ba a makon jiya, abin ya yi wuri a sana’ar da ya runguma
Tsohon dan wasan tawagar Spaniya shi ne ke jan ragamar Al Sadd ta Qatar, tun bayan da ya yi ritaya daga buga wa Barcelona kwallo.
Xavi ya ce babban jami’i Oscar Grau da daraktan wasanni Eric Abidal sun yi masa tayin aikin tun kan a kori Ernesto Valverde ranar Litinin..
Hukumar shirya gasar damban zamani ta duniya ta ayyana watan mayu a matsayin lokacin da za’a dambata tsakanin zakaran danben Duniya Anthony Joshua da dan danben kasar Bulgarian Kubrat Pulev.
Wasan zai gudana dai a filin wasa na Istanbul dake kasar Turkey.
A wasannin sada zumunci da aka buga a jiya a filin wasa na Na’ibawa united tsakanin Basa da man shareef an tashi da ci daya da daya.
A yau kuma Na’ibawa united zata buga ta kungiyar kwallon kafa ta gama emirate a filin wasa na Na’ibawa united a yammacin yau.