Kiwon Lafiya
Rahoto : Najeriya ce ta 4 a masu dauke da cutar Tarin fuka a duniya – WHO
Aisha Sani Bala
Wani bincike da kwararru a fannin kiwon lafiya na hukumar lafiya ta duniya suka gudanar a shekarar 2013 ya gano cewa fiye da mutane miliyan tara ne suka kamu da ciwon tarin fuka a duniya, inda miliyan daya da rabi daga cikinsu suka rasu.
Binciken ya nuna cewa daga cikin wadanda suka kamun akwai mutane dubu dari uku da hamsin masu fama da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV-AIDS.
Ka zalika hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewar Najeriya ce ta 4 a cikin kasashen dake da masu dauke da cutar Tarin fuka.
Ma’anar Cutar tarin fuka : Cutar tarin fuka wadda aka fi sani da TB, cuta ce da ake kamuwa da ita ta hanyar shakar numfashin wanda ke dauke da ita.
Binciken masana ya bayyana cewa ko a nan Najeriya adadin masu dauke da cutar karuwa yake, sakamakon rashin bin ka’idojin da masanan lafiya ke baiwa jama’a domin samun kariya daga cutar.
Freedom Radio ta tattauna da wasu masu dauke da cutar sun, inda suka bayyana irin halin da suka samu kansu a ciki.
“Ina fama da ciwan kirji se ya dunga ci gaba har nafara haki da tari kadan kadan Sai naje asibiti,akayi min gwaji aka tabbatar ina dauke cutar tarin fuka”inda wani Kuma yace”.
“Ina yin tari Sai nai tunaninka na mura ne see Kuma Naga yaki tsayawa said naje asibiti akace tarin fuka nake yanzu mutum biyu a gidanmu suna dauke da cutar”.
Dr Suraj Musa Inuwa likita ne a sashen kula da lafiyar al’umma na asibitin koyarwa na Aminu Kano, ya bayyana irin illar da tarin fuka ke yi ga lafiyar al’umma.
“Babbar illar da take yi a jikin dan adam tana Kama hunhu taci karfinsa takan lalata hunhun idan akayi hoto za aga ya lalace.
Tana Kuma illata kirji da baya har tasan ya mutum ya dunga tafiya a gantsare”
.ya Kuma Kara dacewa”.
Likitan ya kuma kara da cewa allurar rigafin yara da cin abinci mai gina jiki na daga cikin hanyoyin da za su baiwa mutane kariya daga kamuwa da cutar tarin fuka.
“Cin abunci me kyau da yiwa yara rigafi da gujewa shiga cunkoso kasancewa cutar nada babbar alaka da shakar iska me dauke da ita”
Dr Suraj Musa Inuwa ya ce wajibi ne jama’a su rinka kula da tsaftar jikinsu da gujewa shiga cunkoso, kasancewar cutar na da kyakkyawar alaka da shakar iskar da ke dauke da ita.
You must be logged in to post a comment Login