Kiwon Lafiya
Rahoto : Yadda tsaftar mahalli na ma’aikatu da kasuwanni ya kasance a Kano
Daga Madina Shehu Hausa
Gwamnatin jihar Kano ta bukaci dukkanin ma’aikatun jihar da su ci gaba da kula da tsaftace ma’aikatar don Kara fito da martabar jihar a kasar nan.
A yau Juma’a ne ma’aikatar muhalli ta gudanar da zagayen duba tsaftar muhalli na karshen kowanne wata wanda ke zagaya kasuwanni da tashoshin motoci da ma’aikatun gwamnatin, wanda a yau zagayen ya mayar da hankali kan wasu ma’aikatun jihar guda uku.
Kwamishinan muhalli na jihar Kano Dr Kabiru Ibrahim Getso ya yin duban tsaftar na yau Juma’a ya yabawa ma’aikatar kwashe shara ta jihar Kano REMASAB da hukumar kula da zirga zirgar ababen hawa KAROTA har ma da kwalejin koyar da aikin tsafta School of Hygiene sakamakon yadda suka tsaftace ciki da wajen ma’aikatar ta su.
Ta cikin jawabin nasa Dr Kabiru Getso ya ce tun bayan bullar cutar corona aka dakatar da duban tsafatar karshen wata inda aka mayar da hankali wajen yin feshin maganin cutar a guraren cunkoson jama’a.
Ya kara da cewa, kula da tsafatar Muhalli zai taimaka wajen dakile bullar cututtuka da ma yaduwar sa a cikin jama’a.
Ya ce a gobe asabar za’a gudanar da tsaftar muhalli ta du gari, duk da cewa akwai jarrabawar da dalibai ke gudanarwa a goben, inda ya ce sun fito da tsari wajen bai wa daliban damar fita zuwa cibiyoyin rubuta jarrabawar.
Dr Kabiru Ibrahim Getso ya gargadi jama’ar jihar Kano musamman ma direbobin Babura masu kafa uku da su guji fito a yayin da ake tsaftar muhalli.
Da ya ke karbar tawagar tsaftar muhallin, shugaban kwalejin koyar da aikin tsafta ta jihar Kano Dr Bashir Bala Getso, ya ce a kokarin su na tattabar da muhalli mai tsafta makarantar na da tsari mai kyau na inganta muhalli.
Dr Bashir Bala Getso ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta gudanar da feshin magani a makarantar don kuwa dalibai da ke shirin fita daga makarantar na dab da fara rubuta jarrabawa, wanda yin feshin zai tabbatar da kiyaye lafiyar su.
You must be logged in to post a comment Login