KannyWood
Rarara ya yi martani ga masu sukarsa da cewa shi ba ɗan Kano ba ne

Mawakin nan Dauda Kahutu Rarara, ya yi martani ga masu sukarsa da cewa shi ba ɗan Kano ba ne.
A hirarsa da Freedom Radio ya bayyana dalilan da suka sanya aka fi ganin ya fi ɗaukar ɗumi a siyasar Kano.
Rarara ya kuma sake jaddada hasashensa na cewar Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna ne zai lashe zaɓen Gwamnan Kano.
Ya ce, yanzu a siyasar Kano tuni Ganduje ya dame Kwankwaso ya shanye balantana Abba.
Haka kuma ya yi martani ga mawaƙan da suke ganin ba za su iya haɗa hanya da shi ba a siyasa.
Mawaƙin ya kuma yi fida bisa dalilan da suka raba shi da dan takarar gwamna a jam’iyyar ADP Sha’aban Ibrahim Sharaɗa.
Ku kalli cikakkiyar tattaunawar a nan ta hanyar danna alamar Play.
You must be logged in to post a comment Login