Labarai
Rashin fahimta tsakanin ma’aurata ke jawo cin zarafi: Malam Jamilu Ibrahim
Rikicin gida ko rikici tsakanin mata da miji abune da aka dade ana fuskanta wanda a yanzu lamarin ke ka ta’azara
Hayaniya da zagin juna, duka da cin mutunci wani lokaci ma har ta kan kai an rasa rai sakamakon duka na faruwa tsakanin ma’aurata.
Sakamakon bincike da masa halayar dan Adam suka gudanar a lokuta daban daban na nuni da cewar anfi cin zarafin mata akan maza a fadin duniya.
Mafi yawan lokuta a nahiyar Afrika akasari da yawa maza kan yiwa mata dukan kawo wuka kan dalilin da bai kai taka kara ya karya ba , wannan dabi’a ta maza har ta kai da jefa wasu matan a wasu mataki kan dauki mataki ta hanyar ramawa da daukar makamai hakan kuwa kan jawo mutuwar mazajen a idan tsautsayi ya gifta.
Freedom radiyo taji ra’ayoyin wasu mutane kan me ke jawowa matan ake cin zarafin su
Daga cikin su dai wata mata da ta bukaci sakaya sunanta ta bayyana cewa babban dalilin dake haddasa cin zarafin mata bai wuce sa’isa ko kuma fadi-in fada tsakanin miji da mata
Malam Jamilu Ibrahim masani ne akan halayar dan Adam dake koyarwa a jami’ar tarraya dake Dutse a jihar Jigawa ya bayyana dalilin dake jawo rikicin da cewar bai wuce idan mai karfi yayi amfani da karfin sa ba akan wanda yake kasan sa.
Shima wani malamin addini musulunci Malam Adam Muhammad Abubakar ya bayyana illar hakan ta fuskar addini musulunci inda ya ke cewa sabani tsakanin ma’aurata abu ne da ake samu sai dai ya ja hankain ma’aurata da su kasance masu yafiya da juriya tare da fahimtar juna.
Mal Adam Muhammad ya ja hankalin ma’aurata da su san muhimmancin mutunta juna da tsare hakin kowa.