Labarai
Rashin tsaftace baki na kawo bari ga mata masu juna biyu
Wani kwararren likitan hakori da ke asibitin koyarwa na Aminu Kano Dakta Bako Yusuf ya bayyana cewa rashin tsaftace baki na haddasa bari ga mata masu ciki, ko kuma a haifi yaron da hallitar sa bata cika ba, a wasu lokutan kuwa har ma da haddasa rashin haihuwa a tasakanin mutane.
Dakta Bako ya bayyana hakan ne a yayin da ya ke tattaunawa da wakiliyar mu Amina Hamisu Isa a wani bangare na bikin ranar kula da lafiyar Baki ta duniya da ake gudanarwa a yau.
Likitan ya ce yawan ta’ammali da kayan maye da kayan abinci masu zaki na cikin abubuwan da ke haddasa ciwon hakori da sauran cututtukan da suka shafi baki, inda ya ce babbar hanyar da ya kamata mutane su bi wajen magance wannan matsala shine ta hanyar yawan wanke bakin su.
Wasu mutane da muka zanta da su a birnin Kano sun bayyana yadda suke kula da tsaftar bakinsu inda suka a safiyar ko wane rana suna wanke bakin su, inda wasu suka kara da cewa har asuwaki suke don tsaftace bakunan su.
You must be logged in to post a comment Login