Addini
Rasuwar Fafaroma: An ɗage wasanni 4 na gasar Serie A

Hukumar da ke lura da gasar ta Serie A ta ƙasar Italiya, ta sanar da ɗage wasu wasanni na sakamakon rasuwar marigayi Fafaroma Francis.
Rahotonni sun bayyana cewa, wasannin da aka soke sun haɗa da karawar ƙungiyoyin Torino da Udinese Sai Cagliari da Fiorentina da kuma na Genoa da za ta ƙara da Lazio sai kuma Parma da Juventus.
Haka kuma, Hukumar ta sanar da cewa za ta duba wani lokacin da za a buga wasannin a nan gaba.
Kafar yaɗa labarai ta BBC ta ruwaito cewa, tuni ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da dama suka miƙa ta’aziyyar su bisa rasuwar Fafaroma Francis shugaban cocin katolikan na Duniya wanda ya mutu yau Litinin ya na da shekaru 88.
You must be logged in to post a comment Login