Labaran Wasanni
Real Madrid ta lashe laligar Spaniya
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta samu nasarar lashe gasar Laligar kasar Spaniya ta shekarar 2019/2020 a yau Alhamis bayan da ta samu nasara kan kungiyar kwallon kafa ta Villarreal da ci 2-1.
Dan Wasa Karim Benzima ne ya fara zurawa kungiyar tasa ta Madrid kwallo a minti na 29 da fara wasa bayan da ya samu taimako daga hannun dan wasa Luka Modrid sai kuma ya mara ta biyu a minti na 77 a bugun daga kai sai mai tsaron raga, sakamakon keta da akaiwa kyaftin din kungiyar Sagio Ramos.
Yayin da Villarreal ta ci kwallonta Daya ta hannun Dan wasanta Iborra a minti na 84.
Nasarar lashe kofin na Laliga da kungiyar ta Real Madrid tayi a yau ya sanya ta dauki kofin sau 2 cikin shekaru takwas kenan.
Bacerlona dake biyewa kungiyar ta Madrid a matsayin ta 2 a gasar ta Laliga, a wasan data buga yau Laraba da Osasuna ta yi rashin nasara da ci 2-1.
Yanzu dai ya rage wasa daya a karkare gasar ta Laliga inda aka buga wasanni 37 cikin wasanni 38 da za’a yi.
Kungiyar Real Madrid dake matsayin ta daya kuma wadda ta lashe gasar ta Laliga ta hada maki 86 yayin Barcelona dake biye mata a matsayin ta biyu keda maki 79.
Yanzu dai kungiyar kwallon kafar ta Real Madrid za ta mayar da hankalinta a gasar zakarun turai ta Champion league wajen ganin ta doke kungiyar Manchester City dake kasar Ingila a wasan da za su yi zagaye na biyu a ranar 7 ko 8 ga watan Augusta mai kamawa.
A wasan farko dai Real Madrid tayi rashin nasara a hannun Manchester City har gidanta da ci 2-1.
You must be logged in to post a comment Login