Labarai
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 60 a jihar Neja

Rahotanni sun ce wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane da dama bayan sun kai hari kan wani masallaci da kauyukan da ke kewaye da shi a yankin Dekara, ƙaramar hukumar Borgu ta jihar Neja.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya ce maharan sun fara kai hari kauyukan Gidan-Zana da Kpenya kafin su kutsa cikin masallacin Kpenya da misalin ƙarfe biyu na rana ranar Juma’a. Mazauna yankin sun ce an yi garkuwa da sama da mutum 60, duk da cewa ba a tabbatar da adadin ba. Wani da ya tsira daga harin ya zargi ƙungiyar Lakurawa da kai harin.
Kafar yada labarai ta Al’jazeera ta ruwaito cewa, A halin yanzu jami’an tsaro sun tura runduna ta haɗin gwiwa domin gudanar da bincike da aikin ceto. Mazauna yankin sun kuma ce maharan sun sake dawowa a jiya Asabar, tare da dasa nakiyoyi a hanyar fita daga Dekara, inda wata mota da ke ɗauke da wani mutum da iyalinsa ta taka wata nakiyar, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsu.
You must be logged in to post a comment Login