Connect with us

Jigawa

Rikicin Siyasa: Ƴan sanda sun yiwa shalkwatar APC ƙawanya a Jigawa

Published

on

Jami’an tsaro a jihar Jigawa sun kewaye sakatariyar jam’iyyar APC mai mulki a jihar.

Rahotonni sun ce, an wayi gari da ganin jami’an tsaro a kan hanyoyin zuwa sakatariyar jam’iyyar da ke birnin Dutse.

Freedom Radio ta tuntuɓi mai magana da yawun rundunar ƴan sanda ta jihar Jigawa SP. Abdu Jinjiri wanda ya ce, sun girke ƴan sandan ne saboda wasu bayanan sirri da suka samu na yiwuwar afkuwar wani lamari a sakatariyar.

A ranar Litinin da ta gabata ne, gwamnan jihar Alhaji Badaru Abubakar ya jagoranci zama da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar ta APC a fadar gwamnatin jihar, wanda a yayin taron aka da dakatar da shugaban jam’iyya na jihar Alhaji Habibu Sani Sara.

Sai dai kwanaki biyu da wannan taro Alhaji Habibu Sara ya sanar da manema labarai cewa har yanzu shi ne shugaban jam’iyyar APC a jihar.

Habibu Sara ya yi zargin cewa an bijiro masa da wannan batu ne saboda tarayyar sa da wasu mutane da gwamnatin jihar ba ta jituwa da su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 331,772 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!