Labaran Wasanni
Roman Abromovich ya ce zai sayar da kungiyar Chelsea
Mamallakin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dake ƙasar Ingila Roman Abramovich, ya ce a shirye yake da ya sayar da kungiyar.
Abromovich ya bayyana hakan ne a shafin Intanet na kungiyar ta Chelsea a yau Laraba 2 ga watan Maris din shekarar 2022.
Ya kuma ce zai rabar da kudin ne ga al’ummar kasar Ukhraine da yakin da kasar sa ta Rasha ke yi da ita ya shafa.
Abromovic mai shekaru 57 a duniya ya ce a shirye yake ya siyarwa da duk wanda ya bukaci siyan kungiyar a yanzu.
You must be logged in to post a comment Login