Labarai
Rundunar Civil Defense ta nesanta kanta daga karbar cin hanci a hannun masu gidajen Mai
Rundunar tsaro ta Civil Defense shiyyar Kano, ta nesanta kanta da wasu jami’ai da ake alakanta rundunar da su wadanda ake zargin suna karbar cin hanci a daga hannun masu gidajen siyar da man fetur da masu dillancinsa.
hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar DSC Ibrahim Idris Abdullahi, ya fitar da yammacin jiya Lahadi.
Sanarwar ta ce ko kadan ba jami’an rundunar Civil Defense ne ke karbar cin hanci ba kamar yadda aka ankarar da rundunar akan abinda ke faruwa.
DSC Ibrahim ya kuma ce, ”Babu inda Civil Defense ta Kano ta tura jami’anta gurin masu gidajen sayar da man fetur da masu dillancinsa domin su karbi cin hanci da rashawa daga wajen su”
Haka kuma, sanarwar ta ce, yanzu haka kwamandan rundunar Adamu Idris Zakari, yabada umarnin kuma an fara gudanar da bincike domin bankado masu aikata irin wannan cin amana domin daukar matakin shari’a a kansu.
Rundunar ta yi kira ga mutane da su gaggauta kai mata rahoton masu irin wannan dabi’a.
Rahoton: Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa
You must be logged in to post a comment Login