Connect with us

Labarai

Rundunar Soji ta fara aiki da sabbin bataliyoyin dakarunta uku a Zamfara

Published

on

Rundunar Sojin kasar nan, ta fara aiki da sabbin bataliyoyin dakarunta uku a Jihar Zamfara, a wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa ayyukan tsaro da inganta mayar da martani cikin gaggawa.

 

A cikin wata sanarwa da Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar Sojin a Birged ta 1 da ke Gusau, ya fitar a shafin X, ta ce, sabbin bataliyoyin da aka fara aiki da su, su ne Bataliyar Sojojin Ƙasa ta 12 da ke Bakura, da Bataliyar Sojojin Ƙasa ta 23 da ke Kaura Namoda, da Bataliyar Sojojin Ƙasa ta 28 da ke Anka.

 

Ana sa ran bataliyoyin za su faɗaɗa ayyukan rundunar sojin a wuraren da suke gudanar da ayyukansu, tare da tabbatar da tsaron yankunan da aka ɗora musu alhakin kula da su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!