Labarai
Sojoji sun kai wa yan bindiga hare-hare 367 a watan Satumba

Rundunar sojin Najeriya, ta ce, dakarunta sun kai wa yanbindiga hare-hare 367 tare da daƙile wasu a sassa daban-daban na ƙasar a watan Satumban 2026.
Rundunar ta ce Operation Enduring Peace ce, ta fi kai mafi yawan hare-haren, inda takai wa yan bindiga hari 147, sai Operation Fansan Yamma da ta kai hare-hare 115, sannan Operation Whirl Stroke ta kai hare-haren 55.
Daraktan Ayyukan Yaɗa Labaran Tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ya ce sojoji sun mayar da martani a kan hare-haren tare da daƙile maharan.
Onoja Ya ce a cikin watan, sojojin sun kashe ’yan ta’adda da masu aikata laifuka 52, tare da kama wasu 350, sannan suka ceto mutane 655 da aka yi garkuwa da su inda kuma, ’yan tawaye 75 sun miƙa wuya.
Sojojin sun ƙwato makamai 52 da harsasai 2,335, tare da lalata wuraren tace man fetur ba bisa ƙa’ida ba guda takwas.
Sun kuma ƙwato lita sama da 304, da 822 ta man fetur da aka sace.
You must be logged in to post a comment Login