Ƙetare
Rundunar sojin Iran ta sake rufe mashigar Hormuz

Rundunar sojin Iran ta ce ta sake rufe mashigar Hormu saboda ci gaba da toshe tasoshin ruwanta da Amurka ke ci gaba da yi, kamar yadda kafofinyada labaran kasar ta Iran ta rawaito.
Kamfanin dillancin labaran Fars da ke da alaka da dakarun juyin juya halin ƙasar, da kamfanin dillancin labarai na Iran Students da kuma kafar yada labarai ta kasar IRIB, sun rawaito wata sanarwa daga rundunar ta IRGC na cewa mashigin ruwan zai koma “irin yadda yake a baya”, inda dakarun sojin za su ci gaba da tsare mashigar.
A baya mun ga wasu jiragen ruwa na jigilar kaya zuwa hanyar ruwan – amma babu tabbas ko jiragen ruwan soji sun bi ta mashigar ba.
Sanarwar da sojojin ta fitar ta zargi Amurka da “fashin teku”, tana mai cewa “abin da ake rufe mashigar da Amurka ke yi” ya kai fashin teku.
Tun d afarko Iran ta yi barazanar janye matakin da ta ɗauka na buɗe mashigar ga jiragen ruwa, matuƙar Amurka ba ta kawo ƙarshen takunkumin hana jiragenta wucewa da ta sanya a tekun gabas ta tsakiya ba.
Sai dai Shugaba Donald Trump ya dage cewa matakin zai ci gaba da kasancewa har sai an cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin baki ɗaya, yana gargaɗin cewa watakila ba zai sake tsawaita tsagaita wutar da ake ciki ba idan ta kare ranar Laraba.
You must be logged in to post a comment Login