Labarai
Iran ta kai hare-hare a yankin mashigar Hormuz- Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce, Iran ta kai wasu ƙananan hare-hare a yankin mashigin Hormuz, amma bai haifar da babbar illa ga jiragen ruwa ba.
Ya kuma ce Amurka na ci gaba da aikin tsaro domin kare zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin.
Rahotanni sun nuna cewa dakarun Amurka sun lalata wasu ƙananan jiragen ruwan sojin Iran tare da dakile harin makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa da aka kai wa jiragen ruwa na soja da na kasuwanci.
Sai dai Iran ta musanta cewa an lalata jiragenta.
Iran ta bayyana cewa ta yi harbin gargadi ne kawai a kusa da jiragen ruwan Amurka da ke wucewa a yankin.
Wannan rikici ya ƙara tayar da hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, musamman saboda muhimmancin mashigin Hormuz wajen jigilar man fetur da iskar gas a duniya.
You must be logged in to post a comment Login