Labarai
Rundunar sojin Najeriya ta yi sauyin wuraren aiki ga wasu manyan jami’an ta da nufin kara tsaurara tsaro
Rundunar sojin kasar nan tayi sauyin wuraren aiki ga wasu manyan jami’an ta da ke sassa daban-daban da nufin kara tsaurara matakan tsaro a fadin kasar nan.
Wannan na kunshe a wata sanarwa da daraktan sashen hulda da jama’a na rundunar sojin Najeriya Texas Chukwu ya fitar, tare da cewa sauyin wuraren aikin ya shafi jami’an da ke aiki a shalkwatar tsaro da kuma wadanda ke aiki a shalkwatar rundunar dake Abuja.
Sanarwar ta kara da cewa sauyin wuraren aikin ya shafi kwamandojin rundunar Operation Lafiya Dole da kuma na rundunar hadin gwiwa.
Daga cikin wadanda sauyin wuraren aikin ya shafa akwai Manjo Janar A.M Dikko wanda zai kasance a matsayin kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole, sai Birgediya Janar A.O Abdullahi a matsayin mukaddashin kwamandan sashe na biyu na rundunar da sauran su.
Sauran sun hadar da Manjo Janar C.O Ude a matsayin kwamandan rundunar hadin gwiwa da ke Ndjamena da ke Chadi, sai Manjo Janar J. Sarham a matsayin kwamandan runduna ta shida, da Manjo Janar E.B Kabuk da aka tura zuwa runduna ta shida, da Manjo Janar M.S Yusuf babban kwamandan runduna ta tamanin da biyu da sauran su
Daga cikin wadanda sauyin wuraren aikin ya shafa a shalkwatar tsaron da kuma ta rundunar da ke Abuja, akwai Manjo Janar LEO Irabor wanda aka mayar shugaban sashen bayar da horo a shalkwatar tsaro, sai Manjo Janar C.U Agulanna a matsayin shugaban sashen kasafin na rundunar sojin Najeriya da sauran su, inda ake sa ran sauyin wuraren aikin nasu zai fara aiki ne ranar daya ga watan Agusta.