Connect with us

Labarai

Rundunar Sojin Saman Najeriya ta fara shirin daukar sabbin jami’ai

Published

on

Rundunar Sojin Saman Najeriya ta sanar da fara shirin daukar sabbin ma’aikata na bana, ga matasan kasar nan masu sha’awar shiga rundunar a matsayin masu sana’a da wadanda ba masu sana’a ba.

 

Rundunar, ta ce, za a bude shafin neman aikin ta kafar Internet daga ranar 3 ga Satumba zuwa 14 ga Oktoban bana.

 

Haka kuma ta ce, neman aikin kyauta ne, tare da bukatar masu neman shiga aikin na Sojan saman da su karanta sharuddan cancanta kafin cike fom.

 

Rundunar ta ce, masu neman aikin dole ne su kasance tsakanin shekaru 18 zuwa 27, yayin da wadanda ba masu sana’a ba ke bukatar su kasance tsakanin 18 zuwa 22, kana ya zama wajii su kasance ‘yan asalin kasar nan tare da cika ka’idojin lafiya da na jiki da kuma kwakwalwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!