Labarai
Rundunar sojojin Najeriya ta kama mutane 72 da ake zargi da hannu a tashe-tashen hankula a Jos
Rundunar sojojin kasar nan shiyya ta uku da ke garin Jos ta ce ta kama mutane 72 ciki har da mata biyu wadanda ake zargin suna da hannu a tashe-tashen hankula da ke faruwa a jihar Filato da kuma kisan manjo Janar Idris Alkali mai ritaya.
Babban kwamandan operation safe heaven na rundunar da ke aikin samar da tsaro a jihar Filato, manjojanar Augustine Agundu ne ya bayyana haka jiya a garin Jos lokacin da ya ke holen wasu mutane 27.
Ya ce cikin mutane 72 da aka kaman guda 30 sun amince cewa suna da hannu cikin tashe-tashen hankula da ke faruwa a jihar.
Manjo Janar Augustine Agundu ya kuma yi Allawadai da shirun da dattawa da kuma masu fada aji a jihar Filato su ka yi kan tashe-tashen hankula da ke faruwa a jihar, inda ya yi gargadin cewa rundunar ba za ta zura ido tana gani wasu masu neman ta da zaune tsaye suna kaiwan hare-haren ga rundunar ba.
Sai dai wasu mazauna Dura-Du yankin da ake zargin nan aka kashe manjo Janar Idris Alkali sun ce daga shekaran jiya zuwa daren jiya sojojin sun kama mutane sama da dari biyu.
A wani makamancin wannan labari kuma babban hafsan sojin kasa na kasar nan Laftanar Janar Tukur Buratai, ya ce; ‘yan boko da dattawan jihar Filato ne suke daukar nauyin matasa ‘yan tada zaune tsaye a jihar.
Laftanar Janar Tukur Burataiwanda ya samu wakilcin babban kwamandan operation safe heaven da ke aikin samar da tsaro a jihar ta Filato manjo Janar Augustine Agundu ne ya bayyana hakan, yayin jana’izar wasu sojoji uku da ‘yan bindiga suka kashe a ranar shida ga watan jiya na Satumba a yankin karamar hukumar Barikin Ladi da ke jihar ta Filato.
Ya ce akwai kwararan hujjoji da suka alakanta wasu masu fada aji a jihar Filato da rikicin da ke yawan faruwa a jihar, yana mai cewar rundunar za ta dau tsastsauran mataki kan duk wani mutum, komai girman sa don dakile tashe-tashen hankula da ke faruwa a jihar ta Filato.