Connect with us

Labarai

’Yan Sanda sun kama mutane 5 kan zargin sayar da jabun magunguna

Published

on

Rundunar ’Yan Sanda ta kasa  shiyya ta ɗaya da ke nan Kano ta kama mutane biyar bisa zargin sayar da jabun magungunan gargajiya da kuma yin sojan gona da sunan wani mai maganin gargajiya.

 

Wannan na cikin sanarwar da Kakakin Rundunar, DSP Abdullahi Hussaini, ya fitar a ranar Alhamis, 

 

Rundunar ta bayyana cewa, ta kama mutanen ne bayan Dr. Abdulwahab Abubakar Goni Bauchi ya kai ƙorafi, yana zargin wasu da amfani da sunansa, kasuwancinsa da darussansa wajen tallatawa da sayar da jabun magunguna.

 

Waɗanda aka kama su ne Muhammad Usman, Husaini Kabir, Hassan Kabir, Suleiman Salihu da Nura Garba.

 

Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike domin gano tare da kama sauran waɗanda ake zargin suna da hannu.

 

Rundunar ta kuma shawarci jama’a su tabbatar da sahihancin magunguna, masu sayar da su da hanyoyin biyan kuɗi kafin yin ciniki, musamman a kafafen sada zumunta.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!