Labarai
Rundunar ‘yan sanda ta Kano zata fadada bincike a Anambra
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce, za ta yi duk me yiwuwa wajen ganin ta ceto sauran yaran nan talatin da takwas wadanda ake zargin wasu mutane sun sace sun kai su jihar Anambra.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Kano DSP Abdullahi Haruna kKiyawa ne ya bayyana hakan ta cikin shirin duniyar mu a yau, na nan tashar freedom rediyo da ya mai da hankali kan batun ceto wasu yara tara ‘yan asalin jihar Kano a jihar Anambra.
Ya ce, tun bayan samun nasaran ceto yaran, suka fadada binciken su domin gano ragowar.
Kungiyar iyayen yara: ‘ya’ya 47 aka sace mana
Iyayen yaran da aka sace sun bukaci taimakon al’umma
Kano: Yan sanda sun kama wani da ake zargin dan Boko Haram
Daya daga cikin iyayen yaran da aka ceto su, ya shiga tsaka mai wuya lokacin da aka sace ‘yar sa mai suna ‘Amira’ sannan aka sauya mata suna Chinyere yace ya kado matuka da samun wannan labarin
Sakataren kungiyar iyayen yara da suka batan Malam Shuaibu Ibrahim Attajiri cewa ya yi, kungiyar tana iya kokarinta wajen ganin an ceto sauran yaran, nan bada jimawa
A nasa bangaren Malam Ibrahim Khalil kokawa ya yi game da rashin bai wa bangaren tsaro mahimmanci a cewar sa, hakan ya bada gudunmawa wajen faruwar lamarin.