Labaran Kano
Rundunar ‘yan sanda ta yi wawan kamu a Kano
Jami’an rundunar yansandan Jihar Kano ta kama direban Adai-daita Sahu da ake zargin yana jigilar masu kwacen wayoyin salula na hannu ta hanyar amfani da mugan makami.
Kakain rundunar ‘yan sanda ta jihar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya sanar da hakan a yayin zantawa da wakilin mu Abba Isa Muhammadu cewa yana daukar masu kwacen ne ya kuma kaisu guraren da suke tare mutane su zare musu wuka ko almakashi daga bisani kuma sai a su kwace wayar.
DSP Abdullahi Haruna ya kuma kara da cewar cikin wadanda yake dauka aikata mumunan aikin sun hada da Abba Bros da Jiniyo, da kuma Turmi.
Yana mai cewar dukkanin su na zaune a unguwannin Sharada da Tukuntawa a karamar hukumar Birni da kewaye.
You must be logged in to post a comment Login