Labarai
Yan Sandan Sokoto sun cafke mutane 6 da ake zargi da fasa gidaje da sata

Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, ta ce, ta kama mutum shida da ake zargi da hannu a laifukan fasa gidaje, sata da kuma karɓar kayayyakin sata a wasu samame da ta gudanar bisa bayanan sirri.
Rundunar ta ce ta kuma ƙwato babura biyu da aka sace, sai keken ɗinki da kuma wayoyin salula da dama.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Ahmad Rufa’i, ya ce binciken ya biyo bayan rahoton fasa wani gida a unguwar Rumbukawa, inda aka sace keken ɗinki, wayoyi 13 da kuɗade.
A wani samame na daban kuma, rundunar ta ce ta kama wasu mutum uku kan zargin satar babura uku a unguwar Alkammawa, inda ta ƙwato biyu daga cikinsu.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Hassan Shaffa, ya ce rundunar za ta ci gaba da bin duk masu hannu a ayyukan laifi tare da ƙarfafa al’umma su rika bai wa jami’an tsaro bayanan sirri.
You must be logged in to post a comment Login