Tsaro
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani matashi kan zargin garkuwa da wani yaro

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wani matashi Hassan Umar Gwammaja mai shekaru 26, kan zargin garkuwa da wani yaro don neman kuɗin fansa.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a wani sakon murya da ya wallafa a shafin sa na Facebook.
Ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan ya amsa laifin sace yaron a Unguwar Gwammaja, wanda daga bisani aka sako shi bayan biya kudin fansa har Naira miliyan daya.
Matashin da ake zargin mai suna Hassan Umar Gwammaja ya ce matsin tattalin arziki ne yasa shi aikata wannan aiki.
CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce da zarar sun kammala bincike zasu mika wanda ake zargin a gaban kotu.
You must be logged in to post a comment Login