Tsaro
Amurka ta bukaci Ma’aikatar Tsaron kasar ta yi bayani kan hare-haren da Amurkan ta kai Najeriya

Majalisar Dokokin Amurka ta bukaci Ma’aikatar Tsaron kasar (Pentagon) ta yi bayani kan hare-haren saman da Amurka ta kai a Najeriya a ranar 25 ga Disamba, 2025, tare da karin haske kan rawar sojin Amurka a kasar.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa a baya, shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da cewa sojojin kasar sa sun kai hare-hare kan mayakan da ke da alaka da ISIS a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, abinda gwamnatin Tarayya ta ce an yi aikin ne da izininta, kuma bai saba wa ikon kasar ba.
Sai dai a wata wasika da ‘yan majalisar suka aike karkashin jagorancin Sara Jacobs da Jason Crow, sun nemi karin bayani kan doka da aka yi amfani da ita wajen kai harin, hadin gwiwar da aka yi da hukumomin Najeriya, da kuma yiwuwar jikkata fararen hula.
‘Yan majalisar sun kuma nuna shakku kan ikirarin cewa hare-haren sun kai ga ‘yan ISIS, inda suka ce babu kwakkwarar hujja da ke nuna akwai karfin kungiyar a jihar Sokoto.
Rahotanni sun kuma nuna cewa wasu makamai masu linzami sun gaza kai hari yadda ya kamata, inda wasu suka fadi a gonaki da gidajen jama’a, lamarin da ya kara jawo damuwa kan yiwuwar janyo asarar rayuka.
Majalisar ta bukaci Pentagon ta yi bayani kan adadin hare-haren da aka kai, wadanda aka kashe ko suka jikkata, kudin da aka kashe, da kuma shirin Amurka na nan gaba a Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login