Connect with us

Labarai

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga a KH Dawakin Kudu

Published

on

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta sanar da taƙaita zirga-zirga a ƙaramar hukumar Dawakin Kudu, yayin da ake gudanar da zaɓen cike gurbin Majalisar Dokokin jihar a yau Asabar.

 

Rundunar ta ce dokar ta fara aiki ne daga tsakar daren yau zuwa ƙarfe 5 na yamma, domin tabbatar da tsaro da gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali. 

 

Sai dai an ware mutanen da ke gudanar da ayyukan da suka zama dole, ciki har da jami’an INEC, masu sa ido kan zaɓe da aka tantance, ma’aikatan lafiya, da na kashe gobara da ’yan jarida da aka amince da su.

 

Rundunar ta kuma gargadi jama’a kan ɗaukar makamai, saye da sayar da ƙuri’u da kuma yakin neman zaɓe a kusa da rumfunan zaɓe. 

 

Kwamishinan ’yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce duk wanda ya karya dokar takaita zirga-zirga ko wata ƙa’ida ta zaɓe zai fuskanci kamawa da gurfanarwa a gaban kotu.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!