Labarai
Atiku Abubakar ya bukaci Tinubu ya dauki matakin gaggawa wajen rage farashin man fetur

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC a zaben 2027, Atiku Abubakar ya bukaci shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya dauki matakin gaggawa wajen rage farashin man fetur a kasar nan.
Atiku ya ce tsadar man fetur ta wuce matsalar masu ababen hawa, inda ta shafi sufuri, farashin abinci, noma, kasuwanci da kuma kuɗin gudanar da rayuwar yau da kullum.
Da yake jawabi a wani taron manema labarai a Abuja, Atiku ya ce tun bayan cire tallafin man fetur a watan Mayun 2023, ’yan Najeriya na ci gaba da fuskantar karin tsadar rayuwa.
Ya bukaci gwamnatin Tinubu da ta duba tsarin da ya gabatar na bayar da wani nau’in tallafin da za a takaita ga man fetur da tace shi a cikin kasar nan.
Atiku ya ce manufar hakan ita ce rage kuɗin da masu amfani da man fetur ke biya, tare da karfafa samar da man fetur a cikin gida.
Ya kuma ce saura kimanin watanni takwas wa’adin gwamnatin Tinubu ya kare, don haka ya kamata gwamnatin ta mayar da hankali wajen samar wa ’yan Najeriya saukin rayuwa a yanzu, maimakon jiran gwamnati mai zuwa.
You must be logged in to post a comment Login