Labarai
Sabbin sojoji sun kai wa sarkin Kano ziyara
Mai marataba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya shawarci hukumomin asibitin kashi na Dala da su samar da wani sashi wanda zai rika tallafawa marasa karfi da suke neman taimako.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana hakan ne yayin da ya ke karbar jami’an hukumar gudanarwa na asibitin kashi na Dala karkashin jagorancin shugaban asibitin Dakta Muhammad Nuhu Salihu ranar Litinin a fadar sa.
Sarkin ya ce, akwai bukatar samar da sashen tallafawa marasa karfin da suke fama da lalura ta karaya ko kwatankwacin haka a cikin al’umma.
Tun da farko da yake nasa jawabin shugaban asibitin kashi na Dala Dakta Muhammad Nuhu Salihu yace sun samar da wasu bangarori a asibitin da nufin kara inganta aikin asibitin a jihar Kano da kasa baki daya.
Karin labarai:
Limamai su rika hudubar da zata kawo hadin kai Sarkin Kano
Sarkin Kano ya nuna tausayinsa game da halin da al’umma suke ciki
Haka zalika, a yau ne mai Martaba Sarkin Kano ya karbi bakuncin kuratan sojoji dari biyu da hamsin wadanda suka kammala karbar horon aikin soja a fadar sa, a inda yayi musu nasiha da su rike aikin su bisa gaskiya da rikon amana.
Wakilin mu Muhammad Harisu Kofar Nassarawa ya rawaito cewa a yayin ziyarar sojojin sai da su ka yi faretin ban girma a fadar mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.
You must be logged in to post a comment Login