Labarai
Sabon shugaban jami’ar NOUN ya kama aiki
Sabon shugaban Jami’ar karatu daga gida NOUN Farfesa Olufemi Peters ya kama aiki a jiya alhamis, bayan da Farfesa Abdallah Uba Adamu ya kammala aikinsa na shekaru biyar yana jagorantar makarantar.
Wata sanarwa da daraktan yada labaran Jami’ar Ibrahim Sheme ya fitar, ta ce an gudanar da kwarya-kwaryar bikin karbar aikin jiya a shelkwatar NOUN din da ke birnin tarayya Abuja.
Farfesa Olufemi Peters shi ne shugaban Jami’ar na biyar, ya kuma bayyana tsohon shugaban makarantar Farfesa Abdallah Uba Adamu a matsayin jagora na gari da ya dora Jami’ar a kan tafarkin da ya dace na ci gaban ilimi.
A jawabinsa na ban kwana, shugaban Jami’ar mai baring ado Farfesa Abdallah Uba Adamu, godiya ya yi ga Ubangiji da ya ba shi damar shugabantar makarantar, tare da yi wa sabon shugaba fatan smaun nasara yayin jagorancinsa.
You must be logged in to post a comment Login