Labaran Kano
Sai masu hannu da shuni sun tallafa mana – SEMA
Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar kano SEMA ta ce dole ne sai masu hannu da shuni sun shigo cikin hukumar don bada tallafi ga wadanda suka shiga cikin wani iftila’i.
Shugaban hukumar Kwamared Sale Aliyu Jili ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Barka da Hantsi na nan tashar freedom rediyo wanda shirin ya mayar da hankali kan yadda ake samun yawaitar zaftarewar gidaje sakamakon ambaliyar ruwa.
Ya ce yanzu gwamnatoci bazasu iya daukar nauye nauyen wasu mutanen da suka tsinci kan su a halin wani ibtila’i duba da yadda aka samu tabarbarewar tattalin arziki.
Ya kara da cewa jinkirin da akke samu daga hukumar na da nasaba da yadda aka dorawa gwamnati nauyin kowanne abu a bangaren tallafi na kare ibtila’i.
Kwamred Jili yace daga farkon damunar bana zuwa yau an samu ambaliyar ruwa wanda ya tafi da gidaje da gonakin mutane akalla sama da dubu ashirin.
Kwamred Sale Aliyu Jili ya yi kira ga al’ummar jihar kano da su rika gyara magudanan ruwan su domin yin hakan daya ne daga cikin abubuwan da ke takaita barazanar ambaliyar ruwa.
You must be logged in to post a comment Login