Labarai
Sallah Idi : Musulamai su koma kan tafarkin tsira
Masallacin Dakata Malam Salisu Khalid Na’ibi , ya ja hankalin Al’ummar Musulmi kan komawa bisa turbar ma’aiki Salallahu Alaihi wasallam wanda Ubangiji ya umarta kasancewar shine hanyar samun tsira da dacewa.
Malam Salisu Khalid Na’ibi, ya yi kiran ne a hudubar sa da ya gabatar yau Jim kadan bayan kammala Sallar Babbar Idi, wacce ta gudana a Masallacin dake unguwar Dakata.
Na’ibin ya ce duk lokacin da al’umma ta kaucewa umarnin ubangiji, ana jarabtar ta da Annoba wacce hakan na nufin su gyara halayen su tare da kyautata mu’amala kana da komawa ga Allah madaukakin Sarki, bisa yin addu’oi don samun Rahamar sa bisa jagorori na gari.
A nasa jawabin Dagacin Kawaji Alhaji Umaru Adamu, ya yi kira ga al’umma da su bi dukkan ka’idoji da hukumomi suka gindaya na daukan matakan lafiya akan Annobar Cutar Corona, tare kai rahoton duk wani yanayi da basu aminta dashi ba ga hukumomi don kar bata gari suyi amfani da damar wajen cutar da jama’a.
Dumbin al’ummar dake yankin na Dakata da makwabtan ta suka halarci Sallar Idin a Babban Masallacin wanda Na’ibin Masallacin ya yanka Ragon sa na Layya , bayan kammala huduba da Karfe 9 saura na safiyar yau.
You must be logged in to post a comment Login