Connect with us

Coronavirus

Sama da mutum dari biyu sun warke daga Coronavirus a Najeriya

Published

on

Cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta kasa NCDC ta ce mutane 208 ne suka warke daga cutar Covid-19.

Cikin kididdigar da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook a daren jumu’ar nan ta ce izuwa yanzu adadin wadanda suka kamu da cutar sun ka mutum 1095 yayin da 32 daga ciki suka rasu, sai 208 da suka warke sarai daga cutar.

Jihohin dake kan gaba cikin kididdigar jihar Legas ce ta farko mai mutane 657 sai birnin tarayya Abuja dake da mutane 138 yayin da Kano ke biye mata da mutane 73.

Jihar Ogun na da mutane 35, sai ta baya-bayannan da cutar ta bulla wato jihar Gombe inda take da mutane 30, Katsina na da mutane 21.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!