Labarai
Samar da wuraren kiwo zai taimaka wajen samar da ayyukan yi – Kungiya
Kungiyar masu fataucin dabbobi da kayayyakin abinci ta kasa ta bayyana cewa idan har gwmanati za ta samar da wuraren kiwo kamar yadda ta yi ikirari zai taimaka gaya wajen samar da ayyukan yi ga jama’a.
Shugaban kungiyar Malam Muhammad Tahir ne ya bayyana haka ta cikin shirin barka da hantsi na nan freedom radio wanda yayi duba kan yadda ya kamata a kawo zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma.
Malam Muhammad Tahir ya ce samar da ruga da gwmanatin Kano ke kokarin yi lamari ne da zai taimaka wa makiyaya da manoma wajen kyautata sana’oinsu.
A cewar sa kungiyar masu sana’oin fataucin dabbobi da kayayyakin abinci suna taka rawa wajen samar da ayyukan yi ga al’ummar kasa.
Malam Muhammad Tahir ya ce kamata ya yi gwamnati sanya hannu a wannan bangare don bunkasa sanar a gida da kasashen waje.
Ya ce jihar Legas na amfani da dabbobi fiye da dubu guda a kasar nan ya yin da kuma kasahen waje ke son Najeriya ta dinga fita naman dabbobi zuwa ketare.
Amma ya kara da cewar, ‘kasancewar na gida bai koshi ba ya za’a yi a fita da shi’
You must be logged in to post a comment Login