Labarai
Sanata Adamu Bulkachuwa, ya musanta zargin sanya baki a shari’o’in matarsa
Tsohon wakilin shiyyar Bauchi ta Arewa a Majalisar Dattawa, Sanata Adamu Bulkachuwa, ya musanta fahimtar da aka yi masa ta cewa ya taka rawa a wasu hukunce-hukunce da matarsa, Zainab Adam Bulkacuwa ta yanke a lokacin ta na shugabar kotun daukaka kara, inda ya ce an yi wa kalamansa bahaguwar fassara a lokacin da ya alakanta aikin matarsa da majalisa.
Sanatan ya yi kalaman ne a zaman karshe na Majalisa ta 9, inda ya yi ikirarin cewa ya yi amfani da matsayinsa wajen nema wa abokansa ’yan majalisa alfarma a wajen matarsa a lokacin da take rike da shugabancin Kotun Daukaka Kara.
A cewarsa, tsohon shugaban Majalisar Dattawa ne, Sanata Ahmed Lawal ya yanke masa hanzari inda ya rika yi masa katsalandan a lokacin da ya ke bayani.
You must be logged in to post a comment Login