Labarai
Sanya Hijabi: Gwamnan Kwara ya sake rufe wasu makarantu
Gwamnatin jihar Kwara ta yi amai ta lashe kan matakin da ta ɗauka da farko na buɗe wasu makarantu waɗanda ta ba da umarnin rufewa a baya sakamakon saɓani kan ƙyale ƴaƴa mata su sanya hijabi.
A cewar babbar sakatariyar ma’aikatar ilimi ta jihar Kemi Adeosun, ta ce, yanzu an janye komawa makarantun da a baya aka amince su koma karatu a ranar Litinin.
Adeosun ta ce, wannan hukunci an zartar da shi ne da nufin zaman lafiya ga ɗaliban.
A cewar ta, Gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da gaskiya da girmama doka a kan kowane ɗan jihar.
You must be logged in to post a comment Login