Labarai
Sarkin Kano ya bawa matar shugaban Kasa sakon zu Tinubu kan halin matsin da ake ciki
Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi Kira ga gwamnatin tarayya da ta duba da irin halin da al’umma suke ciki na matsin rayuwa, don kawo karshen matsalar.
Sarkin ya bayyana haka ne yayin da ya karbi bakuncin matar shugaban kasa Sanata Remi Tinubu da tawagarta a fadar sa.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce ‘ya kamata matar shugaban kasar ta cigaba da taimakawa mata a bangaren ilimi kamar yanda tayi a jihar Lagos’.
Haka zalika mai martaba sarkin ya shawarci gwamnatin tarayya da tayi duba na tsanaki Kan batun dauke babban bankin kasa CBN da sauran manyan ma’aikatun gwamnatin tarayya zuwa jihar lagos.
Sarkin yace ‘kasancewar jihar kano garin ne mai yawan al’umma da kabilu daban-daban ya kamata gwamnatin tarayya tayi duba wajen kawo cigaba a jihar kano’.
A nata jawabin mai dakin shugaban kasa Sanata Remi Tinubu ta shedawa sarki cewa ‘tazo jihar kano ne domin halartar taro a jami’ar Maryan Abacha da kuma kardamar da wasu aiyuka a jihad kano’.
Freedom Radio ta rawaito cewa “a yayin ziyarar mai dakin shugaban kasa Remi Tinubu ta samu rakiyar matar gwamnan jihar kano da mai dakin shugaban majalisar dattawa da kuma mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau Jibrin da dai sauran jami’an gwamnatin tarayya”.
You must be logged in to post a comment Login