Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sarkin Kano ya bukaci mutane su kada kuri’a kamar yadda doka ta tanada

Published

on

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bukaci al’umma da su fita su kada kuri’a ranar zaben bana kamar yadda doka ta tanada.

Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da ya ke jawabi ga manema labarai a fadar sa.

Alhaji Aminu Ado Bayero, ya Kuma bukaci ‘yan siyasa da su kauce wa neman kuri’u cikin tashin hankali da zubar da jini domin wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Haka kuma ya yi kira ga Hakimai da masu unguwani da su kara sanya ido wajen shige da ficen mutane bakin fuska a yankunan su.

Sarkin, ya kuma bukaci iyaye da su tsawatar wa ‘ya’yansu da su guji shiga hatsaniya.

Alhaji Aminu Ado Bayero,Ya Kuma yi addu’ar Allah, ya sanya a yi zaben lafiya.

 

Rahoton: Shamsu Dau Abdullahi

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!