Labaran Kano
Sarkin Kano ya nuna damuwar sa kan yadda rashin zaman lafiya ya dai-daita Arewa
Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana damuwarsa akan irin yadda rikicin rashin zaman lafiya ya dai-daita al’ummar yankunan Arewa maso gabashin kasar nan.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana hakan ne a yayin da yake karbar tawagar Sarkin Potiskuma Alhaji Umar Bubaram a fadarsa.
Sarkin ya ce babu abinda zai kawar da wannan iftila’in dake faruwa a Arewa maso gabashin kasar nan da ta hada da Yobe da Borno, face komawa ga All…. da kuma dukufa wajen yin addu’oi.
A nasa jawabin Sarkin Potiskuma a jihar Yobe Alhaji Umar Bubaram, ya ce akwai kyakkyawar halaka ta dangantaka mai tsohon tarihi tsakanin Potiskuma da kuma Kano ta tattalin arziki da dai sauran su.
A wani labarin kuma mai martaba sarkin Kano ya nada Salisu Ayuba a matsayin Dagacin garin Karo cikin karamar hukumar Ungoggo, haka zalika sarkin ya nada Umar Abba Muhammad matsayin Mai Unguwar Tudun Makera a karamar hukumar Dala.
Wakilin mu Muhammad Harisu Kofar Nassarawa ya ruwaito a yau aka gabatar da mai Unguwar Kurawa ta cikin birnin Kano wanda ake zargi da kafa gidan kallo a unguwar tasa, dake sanadiyar gurbata tarbiyar matasa.
You must be logged in to post a comment Login