Labarai
Sarkin Kano ya yi kira ga al’umma su bai wa jami’an sunturi hadin kai
Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi kira ga al’umma su dinga baiwa jami’an sunturi gudunmawar da ta dace don dakile matsalar tsaro a kasar nan.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana hakan ne ta bakin wakilin fuskar Arewa a karamar hukumar Dala, Alhaji Sayyadi Muhammad Yola wanda ya wakilce shi ya yin da kungiyar sa kai ta Vigilante ke bude sabon ofishinta a karamar hukumar Dala.
Ya ce, yana da kyau al’ummar gari su rika samar da kayayyakin da za a rika amfani da su don gudanar da aikin tsaro a yankunan su.
A nasa jawabin shugaban kungiyar ta ‘yan sunturi na Vigilante a nan Kano, Muhammad Kabiru Alhaji, ya ce, duba da shigowar damuna ya sanya kungiyar ke kara fadada ofisoshinta a fadin jihar Kano, kuma shi wannan ofishin da aka bude a Unguwar Yalwa zai zama babban ofishin kungiyar a karamar hukumar Dala.
Wakilin mu Abubakar Tijjani Rabi’u, ya rawaito shugaban taron Alhaji Yusuf Ibrahim Wakilin Dukiya, na cewa, ofishin zai yi aiki ne a cikin unguwanni sama da Talatin dake fadin karamar hukumar ta Dala.
You must be logged in to post a comment Login