Labaran Kano
Sarkin Kano ya yi kira ga mawadata su dinga taimakawa marasa karfi
Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci mawadata a cikin al’umma da suka rika tallafawa marasa karfi musamman a wannan lokaci na gabatowar sallar layya da nufin rage musu radadin talauci.
Alhaji Aminu Ado Bayero na bayyana hakan ne a yayin da gidauniyar Dangote ta ke raba kayan masarufi ga mabukata a cikin al’umma a karkashin jagorancin Alhaji Danladi Hanga a fadar mai martaba Sarki.
Sarkin ya ce, irin wannan tallafi ga mabukata yana bukatar a cigaba da aiwatar da irin wannan halaye ga mabukata.
Da yake nasa jawabin Wakilin gidauniyar Dangote a nan Kano Alhaji Danladi Hanga ya ce, gidauniyar Dangote ta shirya bada tallafin ne ga al’umma da nufin taimaka musu a saboda gabatowar babbar sallah.
Wasu daga cikin wadanda suka amfana da tallafin sun bbayana farin cikin su bisa tallafin da suka samu.
Wakilinmu Muhammadu Harisu Kofar Nasarawa ya rawaito cewa daruruwan al’ummma ne suka yi dafifi a Kofar Kudu na gidan sarki don karbar tallafin.
You must be logged in to post a comment Login