Connect with us

Labarai

Sarkin Musulmi ya ayyana ranar Alhamis a matsayin 1 ga watan Safar

Published

on

Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci ta kasa NSCIA, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ayyana ranar Alhamis 16 ga Yulin 2026 a matsayin ranar farko ta watan Safar na shekarar Hijira ta 1448.

 

Hakan na kunshe a cikin sanarwar da Wazirin Sakkwato kuma shugaban Kwamitin ba da Shawara kan harkokin addini na majalisar masarautar Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ya fitar.

 

A cewar sanarwar, Kwamitin ba da shawara kan harkokin Addini tare da Kwamitin kula da ganin wata na kasa ba su samu sahihin rahoton ganin jinjirin watan Safar ba a ranar Talata 14 ga Yulin 2026, wadda ta yi daidai da 29 ga watan Muharram 1448AH.

 

Sanarwar ta ce bisa koyarwar Musulunci, Laraba 15 ga Yulin 2026 za ta cika kwanaki 30 na watan Muharram, kafin a fara watan Safar.

A don haka bisa shawarar kwamitin, Sarkin Musulmi ya amince da ayyana ranar Alhamis 16 ga Yulin 2026 a matsayin ranar farko ta watan Safar Shekara ta  1448 bayan Hijira.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!