Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sarkin Musulmi ya yi watsi da shirin muƙabala da Malam Abduljabbar

Published

on

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III ya yi watsi da shirin Gwamnatin Kano na shirya muƙabalar malamai.

Sarkin ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam da ya ke shugabanta ta fitar ta hannun babban sakataren ta Dr. Khalid Abubakar Aliyu.

Sanarwar ta ce, a baya ta yaba wa Gwamnatin Kano dangane da matakin da ta ɗauka na dakatar da Malam Abduljabbar Kabara daga karatu tare da rufe masallacinsa.

A cewar ƙungiyar, la’akari da kalaman malamin to babu buƙatar shirya wani zaman muƙabala tare da shi.

A ƙarshe JNI ta ce, ita da mambobinta sun cimma matsaya kan cewa, ba za su shiga duk wani taro da aka shirya domin tattauna wa da malamin ba.

Nasril Islam ta ce, tana fata Gwamnatin Kano za ta yi la’akari da wannan matsaya da ta ɗauka domin sauya matsaya.

A ranar Lahadi ne Gwamnatin Kano ta shirya gabatar da wannan muƙabala da ta ce, Mai Alfarma Sarkin Musulmi zai zamo babban baƙo.

Ci gaban wannan labari zai zo nan gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!