Labarai
Yan bindiga sun kai hari garin Adunu da ke jihar Neja

Mazauna yankin Adunu da ke jihar Neja sun wayi gari cikin tashin hankali a safiyar yau 11 ga watan Mayu, bayan rahotannin cewa ƴan bindiga sun shiga garin Kwakuti wanda nan ne mahaifar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Paikoro da Bosso a jihar inda Mazauna yankin ke ci gaba da neman hanyar tsira ta hanyar barin Garuruwan nasu.
Rahotonni sun bayyana cewa ƴan bindigan sun shiga garin Adunu da ke yankin Kwakuti, lamarin da ya sa al’ummar yankin ke ci gaba da tserewa domin neman mafaka.
A halin yanzu, garin Kwakuti ya koma tamkar sansanin masu gudun hijira sakamakon yawaitar mutanen da ke arcewa daga yankunan da rikicin ya shafa.
An tabbatar da kashe mutum guda yayin da wasu suka suka jikkata.
Haka kuma al’ummar yankin na kira ga gwamnati da ta gaggauta turo jami’an tsaro domin dawo da zaman lafiya a yankin.
You must be logged in to post a comment Login