Manyan Labarai
Shah rukh khan ya siyi kyautar bajin ta Filmfire Awards
A ranar Asabar din data gabata ne aka gudanar da bikin bada kyautar bajinta ta FILM FARE AWARDS ga jarumai da masu harkokin Fina-finai a masana’antar shirya finafinai ta India wato Bollywood.
Daga cikin wadanda suka samu kyautar akwai jarumi Ranbir Singh wanda shi ne ya kashe kyautar jarumin jarumai da film din (Gully Boy) sai jaruma Alia Bhat wacce ita ce ta samu nasara a bangaren mata a dai film din na Gully Boy wacce itace ta samu kyautar a shekara da ta gabata ta 2019.
Sai dai a iya cewa bikin bana yabar baya da kura ganin yadda kusan duk a kan film guda daya a ka bada kyautar, domin kuwa mutane da dama na ganin akwai son rai a yadda a ke gudanar da bada kyautar ta Film Fare Award inda suka yi zargin a na amfani da kudi wajen samun kyautar.
Cikin irin mutanen dake kalubalantar yadda bada kyautar ke tafiya akwai wani mai rubuta Waka mai suna Manoj Muntashir, wanda ya rubuta Waka Me taken “Tere Mitti” a cikin film din Kesari na jarumi Akshey Kumar, inda ya ce tabbas akwai lauje cikin nadi kan yadda ake zabar wadanda za a bawa kyautar ta Film fare Awards.
Zargin dai ya cigaba da mamaye kafafen sada zumunta da na yada labaran kasar India bayan da a ka saki wani gajeran bidiyo da ya nuna jarumi (Sha rukh Khan) shi da kansa a wannan bidiyon, inda ya tabbatar da cewa ya taba siyan irin wannan Awards na gwarzon jarumi a shekarar 1993 da Film dinsa mai suna (Baazigar).
Sha rukh khan da tsohon Jarumi Dilip Kumar, su ne jaruman da suka fi samun wannan kyauta ta Film fare Awards.
Jarumi Sha rukh khan, ya ce a wancan lokacin ya na matukar son wannan Award hakan ya sa ya garzaya ofishin daya daga cikin masu tsara kyautar inda ya bashi kudi ya yarda aka zabe shi a matsayin gwarzon jarumi na Shekarar 1993.
Fitar wannan faifan bidiyon dai ya sa mutane da dama na cigaba da kalubalantar ragowar kyautukan bajin ta wato Film fare Awards da jarumi Sha rukh khan ya samu duba da alaka mai karfi dake tsakanin sa da Khaleed Muhammad daya daga cikin alkalan dake fitar da wadanda Suka yi nasara a gasar.
Rubutu : Aminu Abdullahi Ibrahim.