Labaran Kano
Shan Zakami ya yi sanadiyar mutuwar mutane a Kano
Kayayyakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da mutuwar mutane biyu da ake zargin sun sha Zakami a wani gidan biki.
A cewar kakakin rundunar al’amarin afko ne Lamarin dai yafaru ne a makon da ya gabata a Kauyen Tarai a yankin karamar hukumar Kibiya dake nan Kano.
Da yake zantawa da wakilinmu Abba Isah Muhamma, ta wayar hannu Kakakin rundunar yansandan Kano DSP Abdullahi Haruna, ya ce tuni sun kame wadanda ake zargi da hannu wajen hada shi wannan Zakamin wanda aka sanya shi a cikin lemon Sobarodon.
Kazalika rundunar ‘yan sandan ta bakin kakakin ta ce, bayan kama wadanada ake zargin da shan Soborodon su biyar Asibiti ya yin da Allah ya yi wa mutum daga cikin su rasuwa sauran kuma suna samun kulawar jami’an kiwon lafiya.
You must be logged in to post a comment Login