Addini
Sheikh Sudais ya cika shekaru 38 da fara Limanci a Masallacin Harami
Sarki Fahad Bin Abdul’aziz ne ya nada Sheikh Sudais a matsayin limamin masallacin harami na Makkah a shekarar 1984 wanda ya yi daidai da hijira 1404.
An dai haifi Sheikh Abdur Rahman Sudais a birnin Qassim da ke kasar Saudiya 1961.
Shi dai Abdur Rahman Ibn Abdul Aziz As-Sudais fitaccen makarancin alkur’ani ne da ya shahara a duniya ba ya ga kasancewar sa limanin harami da ke birnin Makkah.
A bangare guda shine shugaban kwamitin kula d masallatan haramai guda biyu da ke birnin Makkah da Madina.
Sheikh Sudais dai ya haddace Alkur’ani tun yana dan shekara 12, sannan ya halarci makarantar firamare ta Al-Muthana Bin Harith, inda ya kammala a 1979, inda ya kasance dalibi mafi hazaka a makarantar.
Daga bisani kuma ya halarci jami’ar Riyadh wanda a yanzu ake kira da Jami’ar Sarki Sa’ud, inda ya kammala Digiri a bangaren Sharia a 1983.
Haka zalika, Sheikh Sudais ya ci gaba da karatu, inda ya samu shaidar Digiri na biyu akan shari’a a kwalejin shari’a ta Imam Muhammad Bin Saud da ke jami’ar Musulunci a 1987.
A 1995 ya samu shaidar Digiri na uku a jami’ar Al-Qura, inda ya karanci fannin shari’ar musulunci.
Ya kuma koyar a jami’ar na tsawon shekaru har ma ya kasance daya daga cikin manyan malamai a sashen nazarin shari’ar musulunci.
A shekarar 2016 ne kuma daidai da hijira 1437, Sarki Salman Bin Abdul’aziz ya nada shi a matsayin limamin da zai gabatar da huduba a yayin aikin hajjin shekarar.
You must be logged in to post a comment Login