Connect with us

Labarai

Sheikh Usman Idris Kusfa da aka fi sani da Rigi-Rigi ya rasu

Published

on

Allah ya yi wa shahararren malamin Musuluncin nan Sheikh Khalifa Usman Idris Kusfa wanda aka fi sani da Rigi-Rigi, rasuwa sakamakon fama da jinya da ya yi.

Surikin malamin, Malama Abubakar Ɗanyaro, ne ya tabbatar wa jaridar Aminiya rasuwar malamin, inda ya ce, Sheikh Khalifa Usman Kusfa ya rasu ne a asibiti a daren jiya Lahadi a garin Kaduna.

Abubakar Ɗanyaro ya bayyana cewa sa ran gudanar da Sallar Jana’izarsa a yau Litinin bayan Sallar La’adasar a gidansa da ke unguwar Kusfa a Zariya, bisa koyarwar addinin Islama.

Haka kuma ya kara da cewa, Shehin Malamin, ya yi fama da rashin lafiya tsawon lokaci, inda aka kwantar da shi a Asibiti Sojoji na 44 da ke Kaduna.

Sai dai ya ce, daga baya an mayar da shi wani asibiti mai zaman kansa a unguwar Barnawa a garin na Kaduna inda a nan Allah ya yi masa rasuwa. rayuwarsa da misalin ƙarfe uku da rabi na dare.

Malama Abubakar Ɗanyaro, ya ce, za a gudanar da jana’izar marigayin a yau Litinin da misalin karfe 4:30 na yamma

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!