Addini
Shekara daya kenan cif da rasuwar Abba Kyari
An haifi tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari a garin Maiduguri da ke jihar Borno a ranar 23 ga watan Satumban 1953.
Ya kuma fara karatun boko a makarantar St. Paul College da ke Wusasa a Zari’a.
Abba Kyari ya samu digirinsa na farko kan nazarin zamantakewar dan adam a jami’ar Warwick da ke Ingila a 1980, kafin daga bisani ya kuma yin wani digiri din kan nazarin aikin lauya a jami’ar Cambridge a buraniyar.
Ya kuma halarci makarantar nazarin aikin lauya ta Najeriya 1983
Bugu da kari Abba Kyari ya kuma samu digiri na biyu akan harkar shari’ar a jami’ar Cambride a 1984.
Alakar-sa da shugaba Buhari ta fara ne a 1976 lokacin da Buharin ya ke rike da mukamin gwamnan mulkin soji na jihar Borno.
A watan Agustan shekarar 2015 ne kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nadashi a matsayin mukamin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, mukamin da ya rike har zuwa lokacin mutuwar-sa a ranar 17 ga watan Afrilun 2020.
You must be logged in to post a comment Login