Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Shekarar 2023: Mecece makomar Takai a siyasar Jahar Kano?

Published

on

Tun shekarar 1999 al’ummar jahar Kano suka fara sanin Malam Salihu Sagir Takai bayan dawowa mulkin dumokradiyya a wannan shekarar.

Malam Salihu Sagir Takai ya lashe zaben shugabancin karamar hukumar Takai a karkashin rusasshiyar jam’iyyar APP , a wancan lokaci jamiyyar ta APP tana da kananan hukumomi da basu wuce guda hudu ba a jahar Kano.

A cikin kananan hukumomi 44 na jahar Kano, kananan  hukumomin Fagge da Ungogo da Takai na daga cikin kananan hukumomin da tsohuwar jam’iyyar APP ke mulka.

Amma Malam Salihu Sagir Takai na daya daga cikin fitattun shugabannin kananan hukumomin duk da cewa kananan hukumomi 44 a wancan lokaci na karkashin jamiyyar PDP.

Duk da haka Malam Salihu Sagir Takai ya yiwa karamar hukumar ayyuka da baza su misaltu ba, har sai da ta kai Gwamnan Kano na wancan lokaci Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso na kai ziyara karamar hukumar ta Takai domin nuna ayyuka da Malam Salihu Sagir Takai ya yiwa  karamar hukumar ta sa.

Tsohon gwamnan jahar Kano Malam Ibrahim Shekarau tare da tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso

Bayan faduwar Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso a zaben gwamna na shekarar 2003 sai gwamna Malam Ibrahim Shekaru ya nada Malam Salihu Sagir Takai a matsayin kwamishinan kula da albarkatun ruwa.

Da Malam Ibrahim Shekarau ya sake samun nasara a zaben gwamna na shekarar 2007, ya nada Malam Salihu Sagir Takai mukamin kwamishinan kula da kananan hukumomi.

Likkafar Malam Salihu ta kara habaka , sanda tsohon gwamna Malam Ibrahim Shekarau zai kammala wa’adin sa na gwamna ya goyawa Malam Salihu Sagir Takai baya a zaben shekarar 2011 domin ya gaje shi .

Sai dai kaddara ta saka bai samu nasara a zaben ba, inda tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya lashe zaben.

Amma haka bata sa Malam Salihu Sagir Takai ya karaya ba , a zaben shekarar 2015 ma sai da Malam Salihu Sagir Takai ya tsaya takara amma sai ga shi guguwar canji ta yi awan gaba da Malam Salihu Sagir  Takai ,inda Gwamnan Kano mai ci a yanzu Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yi nasara a kansa.

Malam Salihu Takai ya cigaba da neman Gwamnan jahar Kano, wanda ko a zaben shekarar bana ma sai da ya tsaya amma wannan karo a jam’iyyar PRP, sakamakon canja sheka da yayi daga jami’iyyar PDP.

Amma sanda Malam Takai ya koma jam’iyyar PRP masana harkokin siyasa suna ganin ya Makara , domin ana ganin zaben gumurzu ne tsakanin jam’iyyar APC mai mulkin jahar Kano da kuma ta PDP wadda tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwas ya dawo shi da magoya bayansa.

Tun a zagaye na farko na zaben  ,Malam Salihu Sagir bai samu kuri’u da suka taka kara sun karya ba.

A wannan shekara ta 2019 , sau uku kenan Malam Salihu Sagir Takai ke tsayawa takarar Gwamna, duk da cewa dan siyasa ne da yake da tagomashi na al’umma amma yanayin siyasa na canjawa , wanda dalilan haka ya saka har yanzu Malam Takai bai zama gwamnan jahar Kano ba.

Amma hasashe na nuni da cewa siyasar ubangida na taka rawa wajen samun tagomashi na nasara ko akasin haka, ana ganin raba gari da Malam Salihu Sagir Takai ya yi da ubangidan sa a siyasa kuma tsohon gwamnan jahar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya yi sanadin rashin nasarar sa a siyasa.

Ita dai siyasar jahar Kano masana sharhin siyasa na bayyana ta a matsayin siyasa ta gida -gida tun sanda Najeriya ta dawo mulkin farar hula a shekarar 1979.

Farin jinin dan siyasa na taimakawa wajen nasara da mabiyan sa kan yi.

Wadanda ake ganin suna da gida a siyasar jahar Kano , kuma idan sun nuna yaran su a siyasa sukan lashe zabe.

Ko ma basu lashe zaben ba sukan bawa abokan hamayyar su wahala sakamakon karfin gida na shugabannin siyasar ta su.

Wadanda suka  karfafa gidaje a siyasar Kano da tarin mabiya sun hada da Marigayi Malam Aminu Kano da Marigayi tsohon gwamnan farar hula na farko Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi , sai tsofaffin gwamnonin Kano na jamhuriya ta hudu da muke ciki wato Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso da Malam Ibrahim Shekarau.

Ko gwamnan Kano mai ci a yanzu Dr Abdullahi Umar Ganduje da kyar ya kai a lokacin da ya sake neman gwamnan jahar Kano a karo na biyu a shekarar bana sakamakon raba gari da yayi da tsohon uban gidan sa a siyasa Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso.

Sai da ta kai gwamna mai ci a yanzu ya nemi hada kai da gidan siyasa na Malam Ibrahim Shekarau.

To a yanzu tambayar da masana ke yi  shi ne cewa, shin yanzu Malam Salihu Sagir Takai na kokarin kafa gidan sa ne a siyasance ko kuwa zai sake dawowa gidan tsohon jagoran sa a siyasa Malam Ibrahim Shekarau?

A yadda zaben shekarar 2023 ke karatowa shin siyasar gida za ta kara tasiri, kuma mai Malam Salihu Sagir Takai yake yi na sake damarar tsayawa takarar gwamnan jahar Kano idan Allah madaukakin sarki ya kaimu shekarar ta 2023.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!