Labarai
Shekarau ko Ganduje: Ina Gawuna ya ke?
Fuskar mataimakin Gwamnan Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ta ɓuya a wasu manyan tarukan jam’iyyar APC na Kano.
Yayin da ba a ganshi a taron da Gwamna Ganduje ya shirya ba, haka kuma bai halarci taron da tsohon ubangidansa Malam Ibrahim Shekarau ya jagoranta ba.
A ranar 14 ga watan Oktoban da muke ciki ne Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci taron ƴan amanarsa a siyasa.
Taron ya samu halartar jagororin siyasar Gwamnan da Kwamishinoninsa da kuma ƴan majalisun tarayya dana jihohi waɗanda ke tare da shi, sai dai ba a ga fuskar mataimakinsa ba.
An gabatar da wannan taron ne kwana guda bayan da tsagin tsohon Gwamna Malam Ibrahim Shekarau suka shigar da ƙorafi ga uwar jam’iyyar APC game da yadda Gwamnan ke jagorantarta.
Masu bibiyar al’amuran siyasar Kano sun fassara wannan taro da sunan amsa tayin shata layi tsakanin ɓangarorin biyu.
A taron zaɓen shugaban jam’iyyar APC na jiha da aka gudanar ranar Asabar a ɓangarori biyu, ba a ga fuskar mataimakin Gwamnan ba.
Ƙarin Labarai:
Abdullahi Abbas ne halastaccen shugaban jam’iyya a Kano – APC
Wuta na cigaba da ruruwa a jam’iyyar APC mai mulki a Kano
Me ya sanya ba a ga mataimakin Gwamna ba?
Mun yi ƙoƙari domin jin ta bakin Dr. Nasiru Yusuf Gawuna sai dai haƙanmu bai cimma ruwa ba, kasancewar ba mu same shi a waya ba.
Mun kuma aike masa da saƙonnin kar-ta-kwana wanda har bayan kwana guda bamu samu amsa ba.
Sai dai a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Hassan Musa Fagge ya fitar ya ce, Gawunan ya tafi wakiltar Gwamna Ganduje a wani taron bajakolin kayan gona.
Jama’a da dama na son jin matsayar mataimakin Gwamnan na ko yana tare da Gwamna mai ci, ko kuma ya bi tsohon mai gidansa Malam Ibrahim Shekarau.
Nasiru Gawuna ya shugabancin ƙaramar hukumar Nassarawa sau biyu a lokacin mulkin Gwamna Malam Ibrahim Shekarau.
Wasu ma na zargin cewa, an bai wa Nasiru Gawuna mataimakin Gwamna a zangon farko sakamakon sadaukar da takararsa ta Sanata da ya yi ga Malam Shekarau.
Duka waɗannan tambayoyi muka so samun amsa daga Dr. Nasiru Yusuf Gawuna amma haƙanmu bai cimma ruwa ba.
You must be logged in to post a comment Login